<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 1) Dā can, da Sama ta cika da yabo,
 Nan kuwa zunubi ya ƙaru sosai,
 Yesu ya fito, ya shigo nan duniya,
 Abin godiya,--Jagorana ne.

[V2]
 KORUS
 Kauna ta sa shi ya mutu domina,
 Hukuncina ya kau da shi duk
 Ya baratad da ni, gama ya tashi.
 Yana fa zuwa--ranar daraja.

[V3]
 2) Da aka kai shi kan dutsen Kabari,
 Har aka kashe shi kan giciye.
 Ya sha wahala, da raini da zagi
 Domin zunubanmu, Mai Fansata.
 Korus

[V4]
 3) Da aka binne shi can cikin kogo,
 Aikin ya ƙare, yanzu hutawa.
 Mala'iku suka lura da wurin,
 Begen ƴan Adam, Mai Cetona ne.
 Korus

[V5]
 4) Kabari fa ba ya iya riƙonsa,
 Ƙofa ta buɗe, Yesu ba ya nan,
 Ya ci nasara a kan mutuwa kuwa,
 Yana can Sama, Ubangijina.
 Korus

[V6]
 5) Sai wata rana, ƙaho zai yi ƙara,
 Za a ga ɗaukakar Yesu sosai,
 Tare da tsarkaka, Yesu zai dawo,
 Zan ɗaukaka shi, Yesu nawa ne.
 Korus</lyrics>
<title>Dā Can, da Sama Ta Cika da Yabo LW94</title>
<hymn_number>94</hymn_number>
<author>Traditional, Casting Crowns</author>
</song>